A wasu loquta zaka/ki ga cewa akwai wadanda ba abinda sukayi maka/miki kuma babu wata mu’amala data taba hadaku amma jininku bai hadu ba, haka kurun baka sonsu. To ta yaya zaka/ki ji da irin wadannan mutane? Wadanne hanyoyi zaka/ki bi domin ganin cewa basu gane ka/kin tsane su ba, domin kai/ke kanki/ka baza aso ace sunsan hakan ba. To wannan abu ne mai sauqi idan ka/kin saka kanki.
1. Abu na farko da zaka/ki yi shine duk inda ka/kika san cewa zaku dinga haduwa dashi/ita to ka/ki guji zuwa irin wadannan wurare domin yawan haduwarku ma matsala ne. Koda ace ya/ta zo da niyyar zau yi hira ko magana, ya zama cewa amsoshin da ka/ki ke basu gajeruwar amsa ce. Misali, idan ya/ta ce ‘’ shin ka gane aikin da aka bamu a wurin aiki”? sai ka/ki ce “eh” amma tamabayi Ramatu zata fi iya maka/ki bayani.
2. Abu na biyu idan wannan mutumin mutum ne mai son musu ko jayayya a abubuwan rayuwa, to ka/ki guji yin hakan dashi idan ma ta kama, abu mafi sauqee shine ka/ki ja bakinki/ka ki shuru. Hakan zai saka zai dan dinga tsoron yima wasu abubuwan.
3. Bai dace ba kuma ace idan magana ta kama tsakaninku ka/ki ce baza ka/ki bashi hankalin ki/ka dari bisa dari ba domin kaji bayanin, hakan zai nuna mai cewa baka son sa, wanda zai saka ku shiga wata chakwakiyar kuma, idan ta kama dole sai kun hadu a wurin taron aiki ko wani taron daban to tsakaninka/ki dashi/ita gaisuwa ne kawai, koda sun tambayeka/ki wani abu kamar yadda na fada kada kaja abin yayi tsayi. Ka basu amsar data dace amma wacce bazata basu damar yin wata maganar ba.
Thursday, 26 December 2019
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment