ƙurajen fuska na ɗaya daga cikin ababen da ke ɓata fuska. Aƙwai waɗansu ƙuraje masu yawan naci. Ya kamata mu kula da fuskarmu musamman ma lokacin damina saboda a lokacin ne fuska takan fitar da gishiri watau a turance 'sebum', kamar yadda muka sani, gishirin fuska na toshe ramukan da gumi ke fitowa. Idan hakan ya faru, sai fuska ta fara yin ƙuraje.
Ababen da ake buƙata:
- Kwanuka guda biyu
- ƙwai guda ɗaya
- Takardar 'tissue' guda ɗaya
Amfanin ƙwai ga fuska:
• Ruwan ƙwai na da sinadarin gina jiki da sinadarin bitamin da kuma 'minerals'.
• Yana kare fuska daga ƙuraje.
• Yana kuma rage tsufar fuska.
• ƙarawa fuska haske.
• Rage kumburin ido.
• Yana cire gashin fuska
• Yana matse manyam ramukan fuska
• Ɗaga fatar fuskar data zazzago
• Rage maƙon fuska
• Yaƙar ACNE daga fuska
A samu kwano ɗaya sai a zuba ruwan zafi, wanda da shi ne za'a turara fuskar. Kwano na biyu kuma sai a zuba ruwan ƙwai bayan an cire gwaiduwar, sannan a shafa ruwan 'rose water' saboda samun biyan buƙata.
YADDA ZAKI HADA SHI:
• A fasa ƙwai sai a cire gwaiduwar.
• A kaɗa farin ruwan kwan har sai ya yi kumfa.
• Daga nan sai a shafa ruwan kwan a fuskar musamman ma a kan ƙurajen.
• A yagi takardar 'tissue paper' kaɗan, sai a manna a fuskar daga kan hanci har zuwa kumatu.
• A kara dora wata takardar 'tissue paper' a kan wandda aka manna a fuskar tun a farko, watau hawa biyu kenan.
•Kada a yi dariya ko magana bayan an gama manna takardar 'tissue paper' ɗin, domin yin hakan zai iya buɗe fuska, wadda kuma ana sanya takardar tissue paper ɗin ne don ya matse fuska.
• Bayan haɗin ya bushe, sai a wanke fuskar.
• Sannan sai a shafa gwaiduwar ƙwan a fuska na tsawon mintuna sha-biyar (15). Sannan sai a wanke.
A kula:
Idan kinsan kwai yana kawo miki matsala a fatarki idan kin shafa to kar kiyi amfani dashi wajen gyaran fuska. Wannan matsalar ita ake kira da allergy a turance. Allegy yana kawo ƙuraje, kumburi, wani lokacin da alamun ƙuna.
Idan baki taɓa amfani dashi ba, to sai ki shafa kwan kaɗan a bayan hannunki ko a gwiwarki domin ki tabbatar bazai baki matsala ba.
No comments:
Post a Comment